Yadda Ma’aikata Za Su Daina Jira Kafin Shigowar Albashin Watan Janairu
Manage episode 459513763 series 3311743
A duk lokacin da aka ce an biya albashi, yanayi kan sauya ga masu karba har da masu sana’oi a kasuwanni da kananan shaguna a unguwanni.
Sai dai watan Janairun ko wace shekara kan zo da kalubale kasancewar an biya masu aikin albashi da wuri a cikin watan Disamba, sun kuma karar da shi a kan bukukuwan da watan kanzo dasu.
Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan yadda masu aikin albashi za su kauce wa shiga halin ni-’ya-su kafin biyan albashin watan Janairu
717 afleveringen